1 A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan,
2 aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa.
3 Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”
4 Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.”
5 Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”
6 A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida.
7 Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal.