50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa.
51 Yana cikin tafiya sai ga barorinsa sun taryo shi, suka ce masa, “Ɗanka a raya yake.”
52 Sai ya tambaye su ainihin lokacin da ya fara samun sauƙi. Suka ce masa, “Jiya da ƙarfe ɗaya na rana zazzaɓin ya sake shi.”
53 Sai uban ya gane, daidai lokacin nan ne, Yesu ya ce masa, “Ɗanka a raye yake.” Shi da kansa kuwa ya ba da gaskiya, da jama'ar gidansa duka.
54 Wannan kuwa ita ce mu'ujiza ta biyu da Yesu ya yi, bayan Komowarsa ƙasar Galili daga ƙasar Yahudiya.