12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”
13 Sai suka kai wa Farisiyawa mutumin da yake makaho a dā.
14 To, ran Asabar ne Yesu ya cuɗa ƙasar ya buɗe masa ido.
15 Farisiyawa ma suka tambaye shi ta yadda aka yi ya sami gani. Ya ce musu, “Cuɗaɗɗiyar ƙasa ya shafa a idona, na wanke, ina gani.”
16 Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.
17 Sai suka sāke ce wa makahon, “To, kai fa, me ka gani game da shi, da yake kai ya buɗe wa ido?” Ya ce, “Ai, annabi ne.”
18 Yahudawa kam, ba su gaskata shi makaho ne a dā ba, ya kuma sami gani, har suka kira iyayen wanda ya sami ganin,