6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon,
7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.
8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”
9 Waɗansu suka ce, “Shi ne mana.” Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, kai dai, sun yi kama.” Shi kuwa ya ce, “Sosai ni ne!”
10 Sai suka ce masa, “To, ƙaƙa aka yi idanunka suka buɗe?”
11 Ya amsa ya ce, “Mutumin nan da ake kira Yesu ne ya cuɗa ƙasa ya shafa mini a idanu, ya ce mini, ‘Je ka Siluwam ka wanke ido.’ Na kuwa je na wanke, sai na sami gani.”
12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”