1 Wata rana Jonatan, ɗan Saul, ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye mu je sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai faɗa wa mahaifinsa ba.
2 Saul kuwa yana zaune a karkarar Gibeya a gindin itacen rumman a Migron. Mutum wajen ɗari shida suna tare da shi.
3 Ahaija ɗan Ahitub kuma, ɗan'uwan Ikabod, wato jikan Eli, firist na Ubangiji, yana Shilo, yana sāye da falmaran. Mutane kuma ba su sani ba, ashe Jonatan ya tafi wani wuri.
4 A tsakanin mashigin dutse inda Jonatan yake so ya bi zuwa sansanin Filistiyawa, akwai dutse mai tsayi a kowane gefe. Sunan ɗaya Bozer, ɗayan kuma Sene.
5 Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba.