7 Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.”
8 Sa'an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su.
9 Idan sun ce mana, ‘Ku dakata har mu zo wurinku,’ to, sai mu tsaya cik, ba za mu tafi wurinsu ba.
10 Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”
11 Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”
12 Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.”Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra'ilawa.”
13 Sa'an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su.