1 Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce,“Ubangiji ya cika zuciyata da murna.Ina farin ciki da abin da ya yi.Ina yi wa maƙiyana dariya,Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.
2 “Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji,Babu wani mai kama da shi,Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.
3 Kada ku ƙara yin magana ta girmankai,Ku daina maganganunku na fariya,Gama Ubangiji Allah shi ne masani,Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.
4 An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji,Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi.