1 Aka faɗa wa Dawuda, cewa Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Kaila, suna washe musu hatsi a masussukai.
2 Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?”Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”
3 Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, nan ma a Yahuza muna jin tsoro, balle mu tafi Kaila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa.”
4 Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”
5 Sa'an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Kaila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kashe su da yawa, suka kwashe shanunsu. Da haka Dawuda ya kuɓutar da mazaunan Kaila.
6 Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa.