1 Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa'an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra'ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”
2 Dawuda ya tashi tare da mutum ɗari shida da suke tare da shi zuwa wurin Akish, ɗan Mawok, Sarkin Gat.
3 Dawuda da mutanensa da iyalansu suka zauna tare da Akish a Gat. Dawuda yana tare da matansa biyu, Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail Bakarmeliya, wadda Nabal mijinta ya mutu.
4 Da Saul ya ga Dawuda ya tsere zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.
5 Dawuda ya ce wa Akish, “Idan na sami tagomashi a wurinka, ka ba ni wurin zama daga cikin garuruwanka na karkara domin in zauna a can. Gama me zai sa baranka ya zauna tare da kai cikin birni sarauta?”