1 Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.
2 Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada.
3 Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama'ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake.
4 Ubangiji kuwa ya kira Sama'ila. Sama'ila ya ce, “Na'am.”