6 Ubangiji ya sāke kiran Sama'ila. Sama'ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”
7 (Sama'ila dai bai san Ubangiji ba tukuna, gama Ubangiji bai riga ya fara magana da shi ba.)
8 Ubangiji kuma ya kira Sama'ila sau na uku. Sai kuma Sama'ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Sa'an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron,
9 saboda haka Eli ya ce wa Sama'ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama'ila kuwa ya koma ya kwanta.
10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!”Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”
11 Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Zan yi wa Isra'ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana.
12 A ranar zan cika abin da na faɗa game da Eli da iyalinsa daga farko har zuwa ƙarshe.