23 Amma Dawuda ya ce, “'Yan'uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.
24 Wa zai goyi bayanku a kan wannan al'amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya rabonsu zai zama daidai da juna.”
25 Tun daga wannan rana zuwa gaba, wannan ya zama doka da ka'ida ga Isra'ila.
26 Sa'ad da Dawuda ya komo Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuza, da rabo daga cikin ganimar, ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”
27 Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,
28 da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,
29 da Rakal, da garuruwa na Yerameyeliyawa, da garuruwa na Ƙan'aniyawa,