13 Sa'ad da ya iso, Eli yana zaune a kujerarsa a bakin hanya, yana jira, gama zuciyarsa ta damu saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shiga gari ya ba da labari, dukan garin ya ruɗe da kuka.
14 Sa'ad da Eli ya ji kukan, sai ya tambaya ya ce, “Me ake wa kuka?” Mutumin kuwa ya gaggauta zuwa wurin Eli ya faɗa masa.
15 (Eli yana da shekara tasa'in da takwas, ya kuwa makance ɗungum.)
16 Mutumin ya ce wa Eli, “Yau daga wurin yaƙin na tsere, na gudo gida.”Eli ya ce, “Dana, me ya faru?”
17 Sai wanda ya kawo labarin ya ce, “Isra'ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, an kashe mutane da yawa, har ma da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, sun rasu, an kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
18 Da aka ambaci akwatin alkawari, sai Eli ya tuntsura da baya daga inda yake zaune a bakin ƙofar gari, wuyansa kuwa ya karye, ya mutu, gama shi tsoho ne, mai ƙiba. Ya shekara arba'in yana shugabancin Isra'ila.
19 Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.