19 Surukar Eli, matar Finehas, tana da juna biyu, ta kusa haihuwa. Sa'ad da ta ji labari an ƙwace akwatin alkawarin Allah, surukinta kuma da mijinta sun rasu, sai ta kama naƙuda farat ɗaya, ta haihu.
20 Tana bakin mutuwa, matan kuwa da take taimakonta suka ce mata, “Ki yi ƙarfin hali, gama kin haifi ɗa namiji.” Amma ba ta amsa ba, ba ta kuma kula ba.
21 Sai ta sa wa yaron suna Ikabod, wato ɗaukaka ta rabu da Isra'ila domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma surukinta da mijinta sun rasu.
22 Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra'ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”