1 Akwatin alkawarin Ubangiji ya yi wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.
2 Filistiyawa suka kirawo firistocinsu da bokayensu, suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku sanar da mu yadda za mu komar da shi inda ya fito.”
3 Sai firistocin da bokayen suka ce, “Idan za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila, dole ku aika da kyauta tare da shi domin zunubinku. Ba dama a komar da akwatin alkawarin hannu wofi. Ta haka za ku sami lafiya, za ku kuma san dalilin da ya sa ya yi ta hukunta ku.”
4 Suka ce, “Wace irin hadaya za mu bayar?”Firistocin suka ce, “Sai ku yi marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa, gama annoba iri ɗaya ce ta same ku da sarakunanku.