11 Isra'ilawa suka fito daga Mizfa suka runtumi Filistiyawa, suka yi ta karkashe su har zuwa kwarin Bet-kar.
12 Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki dutse ya kafa shi a tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer, wato “Har wa yau Ubangiji yana taimakonmu.”
13 Ta haka aka ci Filistiyawa. Daga nan ba su ƙara shiga yankin ƙasar Isra'ilawa ba, gama Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa a dukan zamanin Sama'ila.
14 Aka mayar wa Isra'ilawa garuruwan da Filistiyawa suka ƙwace musu, tun daga Ekron har zuwa Gat. Isra'ilawa kuma suka ƙwato dukan yankin ƙasarsu daga hannun Filistiyawa. Akwai kuma zaman lafiya tsakanin Isra'ilawa da Ƙan'aniyawa.
15 Sama'ila kuwa ya yi mulkin Isra'ilawa dukan kwanakin ransa.
16 A kowace shekara yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal, da Mizfa, inda yakan yi musu shari'a.
17 Sa'an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra'ilawa shari'a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.