3 Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”
4 Isra'ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba'al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.
5 Sama'ila kuma ya ce, “Ku tattara dukan Isra'ilawa a Mizfa, ni kuwa zan yi addu'a ga Ubangiji dominku.”
6 Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.
7 Da Filistiyawa suka ji Isra'ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra'ilawa. Sa'ad da Isra'ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,
8 suka ce wa Sama'ila, “Ka yi ta roƙo ga Ubangiji Allahnmu don ya cece mu daga hannun Filistiyawa.”
9 Sama'ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra'ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu'arsa.