19 Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.
20 Ranka ya daɗe, yanzu idanun dukan jama'ar Isra'ila suna kallonka don su ga wanda za ka nuna musu ya gāji gadon sarauta a bayanka.
21 In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”
22 Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo.
23 Aka faɗa wa sarki cewa, ga annabi Natan. Da ya zo gaban sarki, sai ya rusuna ya gaishe shi.
24 Sa'an nan ya ce, “Ranka ya daɗe, ashe, ko ka sanar, cewa Adonija ne zai gaje ka?
25 Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’