7 Ya gama baki da Yowab ɗan Zeruya, da Abiyata, firist. Su kuwa suka yarda su goyi bayansa, su taimake shi.
8 Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.
9 Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.
10 Amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benaiya, ko masu tsaron lafiyar sarki, ko Sulemanu ɗan'uwansa ba.
11 Natan kuwa ya ce wa Bat-sheba tsohuwar Sulemanu, “Ba ki ji cewa Adonija ɗan Haggit ya zama sarki ba? Sarki Dawuda kuma bai sani ba!
12 Yanzu sai ki zo in ba ki shawara domin ki tsira da ranki da na ɗanki Sulemanu.
13 Ki tafi wurin sarki Dawuda, ki ce masa, ‘Ran sarki ya daɗe, ashe, ba ka rantse mini ba cewa, Sulemanu ɗana zai yi mulki bayanka, shi ne kuma zai hau gadon sarautarka? Me ya sa Adonija ya zama sarki?’