1 Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda 'yar Fir'auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa.
2 Suna kuwa cikin al'umman da Ubangiji ya umarci jama'ar Isra'ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna.
3 Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji,
4 sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.
5 Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.
6 Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.