14 Ya yi musu magana bisa ga shawarar matasa ya ce, “Tsohona ya nawaita muku, ni kuwa zan ƙara nawaita muku. Tsohona ya yi muku horo da bulala, amma ni zan yi muku da kunamai.”
15 Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama'a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al'amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.
16 Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!”Jama'ar Isra'ila fa suka tayar,
17 suka bar Rehobowam ya sarauci jama'ar da take zaune a yankin ƙasar Yahuza.
18 Sa'an nan sarki Rehobowam ya aiki Adoniram, shugaban aikin tilas, sai mutanen Isra'ila suka jajjefe shi da duwatsu har lahira. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta, ya hau karusarsa, ya tsere zuwa Urushalima.
19 Da haka mutanen Isra'ila suka tayar wa gidan Dawuda har wa yau.
20 Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.