5 Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.
6 Sarki Rehobowam kuwa ya nemi shawara daga wurin dattawa, waɗanda suka bauta wa tsohonsa, Sulemanu, lokacin da yake da rai. Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan?”
7 Suka ce masa, “Idan za ka zama mai lura da jama'an nan yau, ka bauta musu, sai ka yi musu magana da kyau, su kuwa za su zama talakawanka har abada.”
8 Amma ya yi watsi da shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawara daga wurin matasa, tsararsa.
9 Ya ce musu, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa mutanen nan da suka roƙe ni wai in rage musu nawayar da tsohona ya aza musu?”
10 Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.
11 Zan ƙara a kan nawayar da tsohona ya aza muku. Shi ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”