19 Saboda haka sai annabin ya koma tare da shi, ya ci abinci, ya sha ruwa a gidan tsohon annabin.
20 Sa'ad da suke zaune wurin ci, sai maganar Ubangiji ta zo ga tsohon annabin da ya komar da annabin Allah,
21 sai ya kira annabin Allah, wanda ya zo daga Yahuza, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ba ka yi biyayya da maganar Ubangiji ba, ba ka kuma kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba,
22 amma ka komo, ka ci abinci, ka sha ruwa a wurin da ya ce maka, kada ka ci abinci, ko kuwa ka sha ruwa, saboda haka ba za a binne gawarka a kabarin kakanninka ba.’ ”
23 Bayan da ya ci abinci, ya sha sai tsohon annabin ya ɗaura wa jaki shimfiɗa don annabin da ya komo da shi.
24 Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.
25 Mutane suka wuce, suka ga gawar a kan hanya, da zaki a tsaye kusa da gawar. Suka tafi suka faɗa a birni, inda tsohon annabin nan yake.