11 Duk wanda yake naka wanda zai mutu a birni, karnuka za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura tsuntsaye za su cinye shi, ni Ubangiji, ni ne na faɗa.’
12 “Ki tashi, ki koma gida. Da shigarki birni, yaron zai mutu.
13 Dukan jama'ar Isra'ila za su yi makoki dominsa, su binne shi, gama shi kaɗai zai sami binnewa daga cikin gidan Yerobowam, domin a gare shi kaɗai aka iske abin da Ubangiji, Allah na Isra'ila, yake murna da shi.
14 Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra'ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba.
15 Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.
16 Ubangiji zai rabu da Isra'ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra'ila su yi.”
17 Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.