1 A shekara ta goma sha takwas ta sarautar sarki Yerobowam ɗan Nebat, Abaija ya sarauci mutanen Yahuza.
2 Ya yi mulki shekara uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa.
3 Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba.
4 Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,
5 domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.