19 Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”
20 Sai Ahab ya aika wa dukan jama'ar Isra'ila, ya tattara annabawa ɗin tare da su a dutsen Karmel.
21 Iliya kuwa ya zo kusa da jama'a ya ce, “Har yaushe za ku daina yawo da hankalinku? Idan Ubangiji shi ne Allah, to, ku bauta masa, in kuwa Ba'al ne Allah, to, ku bauta masa.” Mutane duk suka yi tsit, ba su ce uffan ba.
22 Sa'an nan ya ce wa jama'a, “Ni kaɗai ne annabin Ubangiji da ya ragu, amma annabawan Ba'al ɗari huɗu ne da hamsin.
23 To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba.
24 Za ku yi kira ga sunan Ba'al naku, ni kuma zan kira ga sunan Ubangiji. Allahn da ya amsa da wuta, shi ne Allah.”Jama'a duka suka yi sowar nuna yarda da wannan.
25 Sa'an nan Iliya ya ce wa annabawan Ba'al, “Ku zaɓi bijimi guda, ku shirya shi da farko, gama kuna da yawa, sa'an nan ku yi kira ga sunan Ba'al ɗinku, amma fa kada ku kunna wuta. ”