31 Ya ɗibi duwatsu goma sha biyu bisa ga yawan kabilan 'ya'yan Yakubu, wanda Ubangiji ya ce masa, “Za a kira sunanka Isra'ila.”
32 Ya kuwa gina bagade da duwatsun da sunan Ubangiji. Ya kuma haƙa wuriya kewaye da bagaden, za ta ci kamar misalin garwar ruwa guda.
33 Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa'an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.
34 Ya kuma sa a kwarara sau na biyu, suka kwarara sau na biyun. Ya ce kuma a kwarara sau na uku, sai suka kwarara sau na ukun.
35 Ruwa kuwa ya malale bagaden, ya cika wuriyar da aka haƙa.
36 A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.
37 Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”