43 Sa'an nan ya ce wa baransa, “Ka tafi ka duba wajen teku.”Baran kuwa ya tafi ya duba, ya komo ya ce, “Ban ga kome ba.”Sai ya ce, “Ka yi tafiya kana dubawa, har sau bakwai.”
44 A zuwa na bakwai sai ya ce, “Na ga wani ɗan girgije kamar tafin hannu yana tasowa daga teku.”Iliya kuma ya ce, “Tafi, ka faɗa wa Ahab ya shirya karusarsa ya sauka don kada ruwan sama ya hana shi sauka.”
45 Jim kaɗan sai sararin sama ya yi baƙi ƙirin da gizagizai da iska, aka yi ruwan sama mai yawan gaske. Ahab kuwa ya hau karusarsa ya tafi Yezreyel.
46 Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.