1 Ahab kuwa ya faɗa wa Yezebel dukan abin da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe annabawan Ba'al duka.
2 Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”
3 Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza.Ya bar baransa a can.
4 Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
5 Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”
6 Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.