2 Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad,
3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da 'ya'yanka nawa ne!’ ”
4 Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”
5 Jakadun kuwa suka sāke komawa suka ce wa Ahab, “Ben-hadad ya ce, ‘Na aika maka ka ba ni azurfarka, da zinariyarka, da matanka, da 'ya'yanka.
6 Banda haka kuma zan aiko barorina wurinka gobe war haka su bincike gidanka da gidajen fādawanka, su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi da su.’ ”
7 Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”
8 Dukan dattawan da mutane, suka ce masa, “Kada ka kula, balle ka yarda.”