1 Aka yi shekara uku ba a yi yaƙi tsakanin Suriya da Isra'ila ba.
2 A shekara ta uku ɗin, sai Yehoshafat, Sarkin Yahuza, ya ziyarci Sarkin Isra'ila.
3 Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa fādawansa, “Ko kun sani Ramot-gileyad tamu ce, ga shi kuwa, mun yi shiru, ba mu ƙwace ta daga hannun Sarkin Suriya ba?”
4 Ya kuma ce wa Yehoshafat, “Za ka tafi tare da ni zuwa wurin yaƙi a Ramot-gileyad?”Yehoshafat ya amsa wa Sarkin Isra'ila, “Ni da kai ɗaya ne, mutanena kuma mutanenka ne, dawakaina kuma naka ne.”
5 Yehoshafat ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”
6 Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?”Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”