24 Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”
25 Mikaiya ya ce masa, “A ran nan za ka gani, ka kuma gudu ka shiga har ƙurewar ɗaki don ka ɓuya.”
26 Sarki Ahab ya ce, “Ku kama Mikaiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki.
27 Ku ce musu su jefa wannan mutum a kurkuku, a riƙa ciyar da shi da abinci kaɗan da ruwan sha kaɗan, har na komo lafiya.”
28 Mikaiya kuwa ya ce, “In dai ka komo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana da ni ba.” Ya ƙara da cewa, “Kowa ya kasa kunne ga abin da na faɗa.”
29 Ahab Sarkin Isra'ila da Sarkin Yahuza suka tafi Ramot-gileyad.
30 Sarkin Isra'ila kuwa ya ce wa Sarkin Yahuza, “Zan ɓad da kama in tafi wurin yaƙi, amma kai ka sa tufafinka na sarauta.” Sai Ahab ya ɓad da kama ya tafi wurin yaƙi.