44 Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.
45 Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
46 Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.
47 A lokacin babu sarki a Edom sai wakili.
48 Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.
49 Sa'an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.
50 Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.