2 Mutane suka yi ta miƙa hadayu a al'amudai dabam dabam, domin ba a gina haikalin Ubangiji ba tukuna.
3 Sulemanu ya ƙaunaci Ubangiji, ya yi tafiya bisa ga koyarwar tsohonsa, Dawuda, amma ya miƙa sadakoki da hadayu da yawa a al'amudai dabam dabam.
4 Sarki kuwa ya tafi Gibeyon don ya miƙa hadaya, gama a can ne akwai babban al'amudi. Ya miƙa hadayu na ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.
5 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”
6 Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona,domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.
7 Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.
8 Ga ni kuwa a tsakiyar jama'arka wadda ka zaɓa, jama'a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.