7 Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka naɗa ni sarki, a matsayin Dawuda, tsohona, ko da yake ni yaro ne ƙarami, ban ƙware ba.
8 Ga ni kuwa a tsakiyar jama'arka wadda ka zaɓa, jama'a mai yawa wadda ba ta ƙidayuwa saboda yawansu.
9 Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama'arka shari'a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama'arka mai yawa haka?”
10 Ubangiji kuwa ya ji daɗin abin da Sulemanu ya roƙa.
11 Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a,
12 to, zan yi maka yadda ka roƙa, zan ba ka zuciya ta hikima da ganewa har ba wanda ya kai kamarka, ba kuwa wanda zai kai kamarka.
13 Na kuma ba ka abin da ba ka roƙa ba, wato wadata da girma. Domin haka a zamaninka ba za a sami wani sarki kamarka ba.