27 Hakiman nan nasa sha biyu, kowa ya kawo wa Sulemanu abinci, duk da waɗanda suke zuwa teburin cin abincin Sulemanu. Kowane hakimi yakan kawo abincin da za a ci na wata guda. Ba su fasa kawowa ba.
28 Suka kuma kawo sha'ir da ingirci domin dawakan da suke jan karusai, da sauran dabbobin da suke aiki. Kowanne bisa ga abin da aka sa masa.
29 Allah ya ba Sulemanu hikima, da fahimi, da sani, har ba su misaltuwa.
30 Hikimar Sulemanu ta fi ta dukan mutanen gabas, ko masu hikima na Masar.
31 Gama ya fi dukan mutane hikima, ya fi Etan Ba'ezrahe, da Heman, da Kalkol, da Darda, 'ya'yan Mahol. Ya shahara a ƙasashen da suke kewaye da shi.
32 Ya yi karin magana dubu uku, ya kuma yi waƙoƙi fiye da dubu.
33 Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye.