1 A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.
2 Haikalin da sarki Sulemanu ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kamu talatin ne.
3 Tsawon shirayin da yake a gaban Haikalin kamu ashirin ne, wato daidai da fāɗin Haikalin. Fāɗinsa kuma daga gaban Haikalin kamu goma ne.
4 Ya yi wa Haikalin tagogi, suna da fāɗi daga ciki fiye da waje.
5 Ya kuma gina bene mai ɗakuna a jikin bangon Haikalin daga gefe, da kuma bayan Haikalin, har hawa uku, kowanne kamu bakwai da rabi.
6 Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.
7 An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa'ad da ake ginin Haikalin.