31 Ya yi ƙofa biyu na shiga Wuri Mafi Tsarki na can ciki da itacen zaitun. A saman ƙofar ya yi baka.
32 Sai ya zazzāna siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a kan ƙofofi duka biyu, sa'an nan ya dalaye duk ƙofofin da zinariya.
33 Ya yi wa Haikalin madogaran ƙofa masu ƙusurwa huɗu da itacen zaitun.
34 Ya kuma yi ƙyamare biyu a haɗe, ya yi su da itacen fir,
35 ya zazzāna ya adanta su da siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni. Sa'an nan ya dalaye su da zinariya bai ɗaya.
36 Ya gina shirayi na ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al'ul.
37 A shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu aka kafa harsashin ginin Haikalin Ubangiji a watan biyu, wato watan Zib.