11 Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma'auni, da kuma itacen al'ul.
12 Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.
13 Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne.
14 Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.
15 Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi.
16 Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.
17 Ya yi wa kowace dajiya da take kan ginshiƙan ragogi da tukakkun sarƙoƙi. Kowace dajiya tana da guda bakwai.