1 Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.
2 Dukan jama'ar Isra'ila suka taru gaban sarki Sulemanu, wurin biki a watan Etanim, wato wata na bakwai.
3 Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,
4 suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.
5 Sarki Sulemanu kuwa tare da dukan taron jama'ar Isra'ila, waɗanda suka taru a gabansa, suna tare a gaban akwatin alkawari, suna ta miƙa sadakoki, da tumaki, da bijimai masu yawa, har ba su ƙidayuwa.