10 Sa'ad da firistoci suka fito daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya rufe Haikalin Ubangiji,
11 har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.
12 Sa'an nan Sulemanu ya yi addu'a ya ce,“Ubangiji ya ce zai zauna cikingizagizai masu duhu.
13 Yanzu na gina maka ɗaki maidaraja,Wurin da za ka zauna har abada.”
14 Sa'an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama'a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka.
15 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,
16 ‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”