25 Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’
26 Yanzu fa, ya Allah na Isra'ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.
27 “Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!
28 Duk da haka, ya Ubangiji Allahna, ka ji addu'ata, ni bawanka, da roƙe-roƙena, ka ji kukana da addu'ata da nake yi a gabanka yau.
29 Domin ka riƙa duban Haikalin nan dare da rana, wurin da ka ce sunanka zai kasance domin ka riƙa jin addu'ar da bawanka zai yi yana fuskantar wurin.
30 Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.
31 “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,