62 Sa'an nan sarki Sulemanu, tare da Isra'ilawa duka, suka miƙa sadaka ga Ubangiji.
63 Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.
64 A wannan rana kuma ya keɓe tsakiyar filin da yake gaban Haikalin Ubangiji, gama a nan ne ya miƙa hadaya ta ƙonawa, da ta gari, da kitsen sadake-sadake na salama, gama bagaden tagullar da yake gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta ƙwarai da za a yi dukan waɗannan hadayu a kansa.
65 Sa'an nan kuma Sulemanu ya yi biki na kwana bakwai, shi da dukan jama'ar Isra'ila. Mutane suka zo, tun daga Mashigin Hamat a arewa, har zuwa iyakar ƙasar Masar a kudu, suka hallara a gaban Ubangiji Allahnmu.
66 A rana ta takwas ya sallami jama'ar, su kuwa suka yabi sarki. Sa'an nan suka kama hanyar gidajensu suna murna, suna farin ciki saboda dukan alherin da Ubangiji ya yi wa bawansa, Dawuda, da jama'arsa, Isra'ilawa.