9 Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama'ar Isra'ila sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar.
10 Sa'ad da firistoci suka fito daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya rufe Haikalin Ubangiji,
11 har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.
12 Sa'an nan Sulemanu ya yi addu'a ya ce,“Ubangiji ya ce zai zauna cikingizagizai masu duhu.
13 Yanzu na gina maka ɗaki maidaraja,Wurin da za ka zauna har abada.”
14 Sa'an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama'a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka.
15 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,