6 Amma idan kai, ko 'ya'yanka, kun bar bina, ba ku kiyaye umarnaina da dokokina ba, waɗanda na yi muku, amma kuka tafi, kuka bauta wa waɗansu gumaka, kuka yi musu sujada,
7 sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.
8 Wannan Haikali kuwa zai zama tsibin juji, duk wanda zai wuce ta wurin, zai yi mamaki, ya yi tsaki, ya ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi wa ƙasar nan da Haikalin nan haka?’
9 Waɗansu kuwa za su amsa su ce, ‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.’ ”
10 Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.
11 Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.
12 Amma sa'ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba.