2 Ya kuma yi magana da dukan taron Isra'ilawa, ya ce, “Idan kun ga ya yi kyau, idan kuma nufin Ubangiji Allahnmu ne, to, bari mu aika a ko'ina wurin 'yan'uwanmu waɗanda aka rage a ƙasar Isra'ila, mu kuma aika wa firistoci da Lawiyawa waɗanda suke tare da su a biranensu masu makiyaya domin su zo wurinmu.
3 Sa'an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”
4 Jama'a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.
5 Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.
6 Sai Dawuda tare da dukan Isra'ilawa, suka haura zuwa Ba'al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.
7 Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabon keken shanu daga gidan Abinadab. Uzza da Ahiyo suka kora keken shanun.
8 Sai Dawuda da dukan Isra'ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.