2 Daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.
3 Na wajen Yedutun, su ne 'ya'yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji.
4 Na wajen Heman, su ne 'ya'yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot.
5 Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, 'ya'ya maza su goma sha huɗu, da 'ya'ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko.
6 Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki.
7 Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da 'yan'uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne.
8 Sai suka jefa kuri'a domin su ba kowa aikin da zai yi, yaro da babba, malami da almajiri.