8 Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.
9 Shallum yana da 'ya'ya maza da 'yan'uwa, su goma sha takwas jarumawa.
10 Hosa kuma na wajen 'ya'yan Merari, maza, yana da 'ya'ya maza, Shimri shi ne babba, ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka mahaifinsa ya maishe shi babba.
11 Hilkiya shi ne na biyu, da Tebaliya na uku, da Zakariya na huɗu. Dukan 'ya'yan Hosa, maza, da 'yan'uwansa, su goma sha uku ne.
12 Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa.
13 Sai suka jefa kuri'a bisa ga gidajen kakanninsu, ba a damu da yawan jama'a a iyali ba, a kan kowace ƙofar.
14 Kuri'a ta ƙofar gabas ta faɗo a kan Shallum. Sai aka jefa kuri'a don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai kuri'a ta ƙofar arewa ta faɗo a kansa.