1 Bayan rasuwar Saul, sa'ad da Dawuda ya komo daga karkashe Amalekawa, ya yi kwana biyu a Ziklag.
2 Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.
3 Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”
4 Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5 Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”
6 Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.