3 Sai Dawuda ya tambaye shi, ya ce, “Daga ina ka zo?”Ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra'ilawa.”
4 Dawuda ya ce masa, “Faɗa mini abin da ya faru.”Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga bakin dāga, an kuma kashe galibin mutanenmu. Saul da ɗansa Jonatan kuma sun mutu.”
5 Dawuda ya ce wa mutumin, “Ta yaya ka sani Saul da ɗansa, Jonatan, sun mutu?”
6 Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.
7 Da ya waiga, ya gan ni, sai ya kira ni, ni kuwa na amsa, na ce, ‘Ga ni.’
8 Ya ce mini, ‘Wane ne kai?’ Na ce masa, ‘Ni Ba'amaleke ne.’
9 Sai ya ce mini, ‘Zo ka kashe ni gama ina cikin azaba, amma raina bai fita ba.’